Abdullahi ɗan Suhayl
Abdullahi bn Suhayl ya kasance daya daga cikin manyan sahabban Annabi Muhammad S.A.W wanda ya yi hijira zuwa madina ta hanyar amfani da dabara a yakin Badar. Sannan kuma ya kasance dan shahararren dan siyasar kuraishawa , Suhayl ibn Amr kuma dan’uwan Abu Jandal ibn Suhayl[1].
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, 594 (1430/1431 shekaru) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Suhayl ibn Amr |
Sana'a | |
Aikin soja | |
Ya faɗaci |
Expeditions of Muhammad (en) ![]() Badar |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Abdullahi bn Suhayl a shekara ta 594 kuma dan Suhayl bn Amr daga reshen Banu Amir. Mahaifiyarsa ita ce Fakhita bint Amir ibn Nawfal.
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAbdullahi ya musulunta kafin yakin Badar, amma ba shi da hanyar shiga musulmi a Madina. Fita daga Makkah da kasancewarsa musulmi a fili ya yi wa Abdullah wahala saboda tsananin tasirin mahaifinsa da kuma matsayinsa mai daraja a cikin Kuraishawa. Abdullahi ya shirya wani shiri na sauya sheka da hada karfi da karfe da musulmi a Badar. Ya haura zuwa Badar tare da sauran Kuraishawa arna da mahaifinsa, ya jira har sai da rundunonin biyu suka yi sansani kusa da juna, duk suna cikin ganin juna. Da sansanin musulmi ya yi kusa, Abdullah ya tsere zuwa wajen Muhammad ya yi yaƙi tare da su washegari.
Musuluntar da ya yi da wuri da kuma halartarsa a yakin Badar a matsayinsa na musulmi ya sanya shi a matsayi mai kima na Sahabbai. An ce ya yi hijira zuwa Habasha a hijira ta farko. Haka kuma Abdullahi bn Suhayl ya halarci yakin Uhudu, da yakin Rarara, da yakin Yamama.
Mutuwa
gyara sasheAbdullah ya yi shahada a yakin Yamama yana da shekara 38 a shekara ta 632 miladiyya. Surukinsa, Abu Huzaifa bn Utba, dan uwansa, Salim Mawla Abu Huzaifa, da kani na biyu, Zayd bn al-Khattab, duk an kashe su a bayansa. Bayan rasuwarsa, Khalid bn al-Walid ya ce ya cika aikinsa kuma manzon Allah ya yarda da shi a lokacin da ya rasu, ya kuma yi masa addu’a da ya tafi zuwa ga mafi daukaka. Dan uwansa Abu Jandal bn Suhayl da mahaifinsa Suhayl bn Amr sun yi masa makoki sosai. Wani lokaci mahaifinsa ya kan roki Allah ya jikansa da rahama, ya kuma yi wa Abdullahi alheri.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ibn S'ad, Muhammad (1990). Kitab Tabaqat al-Kubra (The Book of the Major Classes) (in Arabic). Beirut: Dar al Kitab Ilmiyya. pp. 310, vol. 3.