Abdulaziz Sani
Abdulaziz Sani Madakin Gini (Yaron Malam) An haifi marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini a shekarar alif 1969, a unguwar Gwangwazo dake jihar Kano. Yayi makarantar framare a makarantar Yelwa daga nan kuma ya hallaci makarantar kimiya da ke a Wudil wato Technical Wudil.
Ya soma harkar rubuce-rubuce a shekarar 1983, wanda rubutunsa ya shafi abin da ya danganci labarai na yaƙi. Littafinsa na farko shi ne ‘Idaniyar Ruwa’ wanda ya wallafa shi a shekarar 1995 daga nan ya rubuta “Duniya Rawar ‘Yanmata da kuma ‘Yaudara Ko Butulci’.
Litttafansa sun yi shura sosai musamman a sanadin ma’aikaci gidan rediyo Muhammad Umar Kaigama.
Manazarta
gyara sasheShuraidDev. (2024, November 6)Tarihin Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin GiniArewanovels.com