Abdulaziz Musa Yaradua
Abdulaziz Musa Yar'adua (an haifeshi a ranar 4 ga watan Augusta, shekara ta 1964)[1] ya kasance dan siyasa ne daga jihar Katsina wanda aka zaba a matsayin sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya a zaben Najeriya na 2023.[2]
Rayuwarsa da karatu
gyara sasheAbdulaziz Musa Yar'adua an haife shi a Katsina ranar 4 ga watan Agusta na shekarar 1964, a garin Katsina. Yayi Makarantar Firamare a Makarantar Musa Yar'Adua Qur'anic Model Primary School a Katsina. Daga 1970 zuwa 1976. Sannan ya tafi makarantar sakandire ta koyan aikin soja da ke zaria (Nigerian Military School) daga shekarar 1976 zuwa 1981.
Daga shekarar 1981 zuwa 1984. Yayi makarantar ilimi mai zurfi ta zaria (College of Advanced Studies) daga nan ya wuce Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zaria, daga 1984 zuwa 1987. Inda ya samu digiri na farko a fannin kimiyya da fasaha.
A shekarar 1991 zuwa 1993 ya tafi kasar Amurka yayi karatun Digiri na biyu (Masters) a fannin harkokin Wutar Lantarki a jami'ar Rochester (USA).
Aiki
gyara sasheYa fara aikin soja a matsayin Kurtun soja har ya samu igiya daya (watau las kofur) kafin ya samu damar yin kwas mai gajeren zango domin samun damar zama ofisa (watau sakan laftanan) a ranar 22 ga watan satumba 1990.
Daga nan sai ya canza zuwa cikakken soja zuwa filin daga a 16 ga watan Maris 1998.
Yayi aiki a karkashin bangaren soja masu aikawa da sakonnin sirri. Ya halarci manyan kwasa-kwasai da tarurruka a fannoni daban-daban na aikin soja da na farar hula, a gida da kuma wajen Najeriya.
Haka kuma ya rike mukaman soja da dama. Tun daga na bada umurni da na sakatare a hukumar soja ta kasa inda ya samu lambobin yabo da dama sakamakon kwarewar sa.
Ya taka matakai da dama har zuwa matsayin laftanar kanar kafin yayi ritaya ta ganin dama a ranar 30 ga watan satumba, 2010, bayan yayi shekaru 29 da wata 4 a aikin soja mai Albarka.
Bayan ritayar da yayi, ya shiga cikin harkokin siyasa don cigaba da bada gudummuwa ga kasa da al'umma.
Daga farko, ya shiga jam'iyar CPC a shekarar 2010 zuwa 2013 bayan zabe na 2011, sai aka samu hadin kai tsakanin jam'iyarsu da sauran jam'iyyun adawa, aka samar da jam'iyar APC.
Yayi rijista a jam'iyyar APC a shekarar 2014. Yayi takarar Gwamna, da takar kujerar dan Majalisar tarayya ta katsina, a shekara 2015, bai samu nasara ba.
A shekarar 2019, yayi takarar kujerar sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya shima bai samu nasara ba.
Jam'iyyar APC ta nada shi a matsayin sakatare da mataimakin sakatare da kuma mamba na komitocin zartarwa daban daban sakamakon jajircewar shi da aiki tukuru.
Ta wadannan hanyoyin da sauransu, ya bada gaggarumar gudunmmuwar samun nasarar Jam'iyyar APC a jihar Katsina da kasa baki daya.
A watan Fabreru na shekarar 2022, Shugaban kasa Muhammadu buhari ya bashi mukami na chairman na Ma'aikatar sa wutar lantarki ga kawyukan Nigeria (watau Rural Electrification Agency). Ya aje wannan mukami don tsayawa takarar zaben fitar da gwani na Sanatan katsina ta tsakiya, kuma Allah ya bashi nasara.
Ya kuma samu nasarar lashe babban zaben Sanatan Katsina ta tsakiya da hukumar INEC ta sanar a ranar 27 ga watan Febreru 2023.
Haka kuma yana rike da Sarautar Mutawallen Katsina da Akajiugo 1 na Rzeokwe Kingdom,
Ibagwa Nike (Enugu). Yana da iyali da yaya bakwai.