Abdul Rasheed Baloch (an haife shi a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara 1972) Dan wasan Olympics ne kuma ƙwararren dan dambe a kasar Pakistan. A matsayinsa na mai son, ya kasance kyaftin din kasar Pakistan a shekara ta 1997 zuwa shekara ta 1998. Ya shiga cikin Wasannin gasar Olympics a shekara ta 1996; ya lashe gwagwarmayarsa ta farko da dan wasan dambe na Mexico kuma ya rasa wasan sa na biyu da dan wasan Kazakhstan a cikin kilo 67.[1][2] 

Abdul Rasheed Baloch
Rayuwa
Haihuwa Hyderabad (en) Fassara, 8 ga Afirilu, 1972 (52 shekaru)
ƙasa Pakistan
Sana'a
Sana'a boxer (en) Fassara
Nauyi 67 kg
Tsayi 175 cm

A shekarar 1995 ya lashe gasar:

  • Azurfa a cikin Wasannin Kudancin Asiya shekara ta 1995;
  • Zinariya a gasar cin kofin Agon, kasar Malaysia;
  • Zinariya a gasar cin kofin duniya ta Quaid-i-Azam;
  • Azurfa a cikin Kofin KESC;
  • Bronze a gasar Giraldo Cordova Cardin ta Duniya, Cuba;
  • Azurfa a cikin Green Hill Cup, kasar Pakistan .

Manazarta

gyara sashe
  1. Shafi, Faisal (8 January 2021). "10 Famous Pakistani Boxers In The Ring". DESIblitz. Retrieved 31 August 2024.
  2. Muhammad, Nigah (4 July 2022). "Wish young boxers avoid arduous path I have treaded: Olympian Rasheed Baloch". MM News. Retrieved 31 August 2024.