ADABIN BAKA NA MAGANGANUN AZANCI

ADABIN BAKA NA MAGANGANUN AZANCI

Matsayin Ta tsuniya

Ta tsuniya aba ce ta gargajiyar Hausawa wacce suke hulɗa da ita don koyawa ƴaƴansu wasu darussa na ilimin zaman duniya, kuma labarai ne ƙagaggu ake haɗawa a tayar da gangan jikin ta tsuniya.

Tubalin Ginin Ta tsuniya

Tubali su ne abubuwa da ake haɗawa a tayar da gangan jikin tatsuniya, daga ciki akwai misalai kamar;

1- Mutane: Sarki, Galadima, ko Waziri, ko Ɗansarki, ko Ƴarsarki, Boka, ko Jakadiya, Miji da Mata, Mowa da Gora da Kuturu da Makaho da Makiyayi da sauransu.

2. Dabbobi: Kamar Zomo, Dila, Zaki, Kura, Kurege, Damo, Biri, Giwa, Raƙumi, Mariri, Barewa, Damisa, da sauransu.

3- Tsuntsaye da Ƙwari: Kaza, Zakara, Balbela, Hankaka, Kurciya, Jimina, Zalɓe, Tantabara, Maciji, Kunama da sauransu.

4- Aljanu: Doguwa, Ɗantsatsunba, Hash-Hash, Maifitila da sauransu.

Bayan waɗannan, tatsuniya takan ƙunshi kamar su; Gizo, Ƙoƙi, Dodo, Fatalwa, duk kuwa waɗannan ƙirƙirarrun abubuwa ne.

NAU'OIN TA TSUNIYA

Tatsuniyoyin Hausa sun kasu biyu kamar haka;

-Tatsuniyar Gizo, Ita ce wacce sunan Gizo ya fito a cikin tauraro da matarsa Ƙoƙi mai taimaka masa.

-Sauran Tatsuniyoyi, su ne wadda mutane da dabbobi ko tsuntsaye, aljanu ko dabbobi ke fitowa a matsayin taurari.

JIGOGIN TATSUNIYA

Daga cikin darussan da Tatsuniyoyi ke koyarwa akwai; Tarbiya, haƙuri, tausayi, biyayya, halaye na gari, da wayo, da nishaɗantarwa, da kauce miyagun halaye, da sauransu.

MUHIMMANCIN TA TSUNIYA

1. Koyawa yara tarbiya

2. Hana yara yawon banza

3. Ishara kan gujewa miyagun halaye

4. Taskace kalmomin Hausa

5. Ƙarawa yara basira