ABUBUWAN DA AKE SO MUSULMI YA YI KAFIN SALLAR IDI

ABUBUWAN DA AKE SO MUSULMI YA YI KAFIN SALLAR IDI

gyara sashe

Tabbatuwar Sallar Idi:

gyara sashe

Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da su (Ƙaramar Sallah da Babbar Sallah) kowacce ta tabbata a shara'i, ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.

Tabbatuwar Babbar Sallah:

Ita kuma sallah ce da ake gabatar da ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Ita ma babbar Sallah ta tabbata a Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah maɗaukakin sarki yake cewa ''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (abin hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada Sallah da Yanka, a ayar kamar wacce ta gabata an haɗa Zakka da Sallah.

Wannan tabbatuwar wadannan sallolin, a ayoyin Alƙur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud da Nasa'i duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace,

''Na harci Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sai ya fara gabatar da sallah kafin Huɗuba ba tare da an yi kiran sallah ba aka tada Ikama''.

Haka shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana huɗuba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace ''Duk wanda ya yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin namu to yankanshi ya yi daidai, wandako ya yanka kafin ayi sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''. Wannan hadisin Malaman Hadisai bakwai ne suka ruwaito shi.

Wankan zuwa Idi

Wankan zuwan Idi Sunnah ne. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma'a.

Sanya tufafi masu kyau

Wannan al'ada ce da Musulunci ya tabbatar da ita. Kuma sunnah ce ga musulmi ya saka tufafi sabo mai kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare.

Idi ranar bayyana farin ciki ne da godiya ga Allah a kan ni'imar da ya yi wa bayinsa na yin Arfa.

Zikiri yayin tafiya zuwa masallacin Idi

Ana son a yi ta yin kabbara a yayin tafiya Idi har idan an zauna a filin Idi zuwa sai liman ya zo.

Mai tafiya idi zai dinga cewa: "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar," ko kuma ya ce " Allahu Akbar, Allahu Akbar, Lailaha illahahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd.

Ana kuma cewa: "Allahu Akbar Kabira Walhamdu lillahi kasira, Walhamdulillahi bukratan wa asila."

Za a daina kabbara idan Liman ya tayar da sallah.

Ba a sallar nafila a filin idi

Sallar Idi ba ta da Nafila domin ita ma Nafila ce. Amma idan a cikin masallaci ne za a yi Idi watakila saboda ruwan sama, to mutum yana iya nafilar gaisuwa ga Masallaci.

Amma a filin Idi ba a nafila. Mutum yana zuwa zai zauna kuma ya ci gaba da kabbara har isowar liman.

Sauraron huɗuba bayan sallar idi

Ana huɗubar Idi bayan sallame Sallah. Ana son a zauna a saurari hudubar Liman, ba a son daga sallame sallah a fice.

Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malamai sun ce yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huɗuba.

Sauya hanyar tafiya da dawowa

Wannan Sunnah ce ta Manzo SAW ba a son a tsayar da hanya daya. Ana son mutum ya sauya hanya idan zai dawo daga Idi domin zai yi wa wasu mutane na daban sallama sabanin wadanda ya yi wa sallama a lokacin tafiyarsa.

Yara da mata da tsoffi duka na zuwa Sallar idi

Ana son dukkan al'umma su tafi idi, maza da mata da yara da tsoffi. Mata masu haila za su iya zuwa amma ba za su shiga sahu ba, za su tsaya a gefen masallaci.

Ana son mata idan za su tafi idi su suturta jikinsu, ka da su tafi Ibadah suna bayyana jiki kuma suna bayyana adonsu. Sannan ba a son mata su jera sahu daya da maza a filin idi. An fi son maza suna gaba mata na baya.

[1]

  1. https://www.bbc.com/hausa