A'antawa
Kalmar A’antawa, samammiya ce daga a’a, wacce ke da ma’ana ta kore aiki ko wani abu; abin nufi shine cewa, tana nuna rashin samuwa ko faruwar wani abu. Misali: Wancan gida ne, wancan ba gida ba ne.
Idan muka lura da jimlar farko “Wancan gida ne”, za mu ga cewa ta nuna samuwar gida a wani bangare da ake iya hangowa. Jimla ta biyu kuma “Wancan ba gida ba ne”, ta kore samuwar gidan da ake magana a kansa. Saboda haka wannan jimla ta biyu ta a’antar da jimlar farko.
Ga kuma wani misali a cikin magana: Ado, kai ne ka zubar da wannan ruwan? A’a. Wannan kalma da Ado ya bayar da amsa da ita, ita ake ɗafawa “ntawa” a goshinta sai ta zama a’antawa duk kuwa da cewa tushen/saiwar kalmar ita ce a, ta zama a’a, sannan aka yi mata ɗafiyar ntawaa goshi ta koma a’antawa.
Ƙa’idojin A’antawa
gyara sasheƘa’ida ita ce abar da ke jan ragamar kowane lamari ya tafi yadda ya kamata sannan kuma bai ɗaya a kowane bigire sannan kuma a koda wane lokaci. A’antawa ma ba a barta a baya ba.
Kalmomin a’antawa: Ana a’antar da zance da kalmomin ba, kada, da maras.
A’antawa da Lokutan Aikatau
gyara sasheAna amfani da a’antau ba ta sigar ba……ba wajen a’antar da lokutan aikatau masu zuwa:
Shuɗaɗɗen Lokaci: Shi ne aikin da ya wuce. Misali:
- Kura ta wuce. Ba kura ce ta wuce ba.
- Ka karanta. Ba ka karanta ba.
- Sun sayar. Ba su sayar ba.
Lokaci na yanzu: Shi ne aikin da ke faruwa a lokacin da ake magana. A wannan yanayin ana amfani da a’antau ba, sannan sai kuma wakilin suna ya biyo bayanta. Saɓanin yadda muka gani a baya. Misali:
- Suna magana. Ba sa magana.
- Yana cin abinci. Ba ya cin abinci.
Sababben lokaci: Shi ne aikatau ɗin da ke nuna aikin da aka saba yi. Da ba……ba ake a’antar da shi. Misali:
- Kukan zo tare. Ba kukan zo tare ba.
- Yakan wanke hula. Ba yakan wanke hula ba.
- Takan kula shi. Ba takan kula shi ba.
Lokaci Na Gaba Na I: Shi ne lokaci mai zuwa nan gaba. Ana a’antar da shi da ba……ba. Misali kamar haka:
- Za su tafi. Ba za su tafi ba.
- Za mu hau jirgi. Ba za mu hau jirgi ba.
- Za ka mayar. Ba za ka mayar ba.
- Za ta dafa tuwo. Ba za ta dafa tuwo ba.
Lokaci Na Gaba Na II: Lokaci mai zuwa. Ana a’antar da shi da ba…..ba. Misali:
- Taa rubuta shi. Ba taa rubuta shi ba.
- Maa nuna masa. Ba maa nuna masa ba.
Umarni: Ita ce kalmar aikatau da ke nuna umarni. Ana a’antar da ita da a’antau kada. Misali:
- Yi dariya. Kada ka yi dariya.
- Fice daga nan. Kada ki fice daga nan.
- Ku tafi. Kada ku tafi.
Siffa
gyara sasheAna a’antar da siffofin mai da masu ta hanyar juya su zuwa maras da kuma marasa. Kalmar mai, tana siffanta namiji ko mace mamallaki wani abu guda ɗaya. Jama’unta ita ce masu. Misali:
- Mai mutunci Maras mutunci.
- Masu mutunci Marasa mutunci.
- Mai hankali Maras hankali.
- Masu hankali Marasa hankali.
Ɗauraya
gyara sasheA’antawa ita ce kore abu. Kalma ce da ta samo asali daga a’a, wacce aka yi wa ɗafiya a goshi da ntawa. Ana amfani da kalmomin ba, kada, marasda marasa wajen a’antar da zance. Ita ba, tana da sigogi guda biyu; ba da take aiki da lokaci na yanzu, sai kuma ba…………ba, wacce take aiki da shuɗaɗɗen lokaci, lokaci na gaba I da II, da kuma sababben lokaci. Kada, tana a’antar da umarni. Daga ƙarshe kuma, sai maras da marasa da suke a’antar da siffa a jinsin namiji da mace, tilo da jama’u. Marasa, ita ce take ɗaukar jama’u.
Manazarta:
gyara sasheSani M.Kalmar a’antawa, samammiya ce daga a’a, wacce ke da ma’ana ta kore aiki ko wani abu; abin nufi shi ne cewa, tana nuna rashin samuwa ko faruwar wani abu. Misali: Wancan gida ne, wancan ba gida ba ne.
Idan muka lura da jimlar farko “Wancan gida ne”, za mu ga cewa ta nuna samuwar gida a wani bigire da ake iya hangowa. Jimla ta biyu kuma “Wancan ba gida ba ne”, ta kore samuwar gidan da ake magana a kansa. Saboda haka wannan jimla ta biyu ta a’antar da jimlar farko.
Ga kuma wani misalin a cikin magana: Ado, kai ne ka zubar da wannan ruwan? A’a. Wannan kalma da Ado ya bayar da amsa da ita, ita ake ɗafawa “ntawa” a goshinta sai ta zama a’antawa duk kuwa da cewa tushen/saiwar kalmar ita ce a, ta zama a’a, sannan aka yi mata ɗafiyar ntawaa goshi ta koma a’antawa.
Ƙa’idojin A’antawa
gyara sasheƘa’ida ita ce abar da ke jan ragamar kowane lamari ya tafi yadda ya kamata sannan kuma bai ɗaya a kowane bigire sannan kuma a koda wane lokaci. A’antawa ma ba a barta a baya ba.
Kalmomin a’antawa: Ana a’antar da zance da kalmomin ba, kada, da maras.
A’antawa da Lokutan Aikatau
gyara sasheAna amfani da a’antau ba ta sigar ba……ba wajen a’antar da lokutan aikatau masu zuwa:
Shuɗaɗɗen Lokaci: Shi ne aikin da ya wuce. Misali:
- Kura ta wuce. Ba kura ce ta wuce ba.
- Ka karanta. Ba ka karanta ba.
- Sun sayar. Ba su sayar ba.
Lokaci na yanzu: Shi ne aikin da ke faruwa a lokacin da ake magana. A wannan yanayin ana amfani da a’antau ba, sannan sai kuma wakilin suna ya biyo bayanta. Saɓanin yadda muka gani a baya. Misali:
- Suna magana. Ba sa magana.
- Yana cin abinci. Ba ya cin abinci.
Sababben lokaci: Shi ne aikatau ɗin da ke nuna aikin da aka saba yi. Da ba………ba ake a’antar da shi. Misali:
- Kukan zo tare. Ba kukan zo tare ba.
- Yakan wanke hula. Ba yakan wanke hula ba.
- Takan kula shi. Ba takan kula shi ba.
Lokaci Na Gaba Na I: Shi ne lokaci mai zuwa nan gaba. Ana a’antar da shi da ba………ba. Misali:
- Za su tafi. Ba za su tafi ba.
- Za mu hau jirgi. Ba za mu hau jirgi ba.
- Za ka mayar. Ba za ka mayar ba.
- Za ta dafa tuwo. Ba za ta dafa tuwo ba.
Lokaci Na Gaba Na II: Lokaci mai zuwa. Ana a’antar da shi da ba…..ba. Misali:
- Taa rubuta shi. Ba taa rubuta shi ba.
- Maa nuna masa. Ba maa nuna masa ba.
Umarni: Ita ce kalmar aikatau da ke nuna umarni. Ana a’antar da ita da a’antau kada. Misali:
- Yi dariya. Kada ka yi dariya.
- Fice daga nan. Kada ki fice daga nan.
- Ku tafi. Kada ku tafi.
Siffa
gyara sasheAna a’antar da siffofin mai da masu ta hanyar juya su zuwa maras da kuma marasa. Kalmar mai, tana siffanta namiji ko mace mamallaki wani abu guda ɗaya. Jama’unta ita ce masu. Misali:
- Mai mutunci Maras mutunci.
- Masu mutunci Marasa mutunci.
- Mai hankali Maras hankali.
- Masu hankali Marasa hankali.
Ɗauraya
gyara sasheA’antawa ita ce kore abu. Kalma ce da ta samo asali daga a’a, wacce aka yi wa ɗafiya a goshi da ntawa. Ana amfani da kalmomin ba, kada, marasda marasa wajen a’antar da zance. Ita ba, tana da sigogi guda biyu; ba da take aiki da lokaci na yanzu, sai kuma ba…………ba, wacce take aiki da shuɗaɗɗen lokaci, lokaci na gaba I da II, da kuma sababben lokaci. Kada, tana a’antar da umarni. Daga ƙarshe kuma, sai maras da marasa da suke a’antar da siffa a jinsin namiji da mace, tilo da jama’u. Marasa, ita ce take ɗaukar jama’u.
Manazarta:
gyara sashe- ↑ Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan – Nigeria. Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan – Nigeria. A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan – Nigeria. Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.