‘Yan matan Dakh
Dakh Daughters wani gangami ne na, na waka da wasan kwaikwayo a Ukraine wanda aka fara a 2012 a Kyiv. Ƙungiyar ta ƙunshi mata bakwai, waɗanda ke wasa da kayan kida daban-daban kuma suna rera waƙa a cikin harsuna daban-daban (Harshen Ukraine, Turanci, Faransanci, Jamusanci,Rashanci) da sauran yarukan kasar Ukraine. [1] Suna yawan amfani da rubutun shahararrun marubuta a cikin waƙoƙinsu (misali Taras Shevchenko, William Shakespeare, Joseph Brodsky, Charles Bukowski, Shaggy ).
‘Yan matan Dakh | |
---|---|
musical ensemble (en) | |
Bayanai | |
Work period (start) (en) | 2012 |
Location of formation (en) | Kiev |
Nau'in | folk music (en) da cabaret (en) |
Shafin yanar gizo | dakhdaughters.com |
'Yan matan Dakh membobi ne na ayyuka daban-daban irinsu DakhaBrakha da Perkalaba . Sunan ƙungiyar ya samo asali ne daga gidan wasan kwaikwayo na Dakh wanda ke da alaƙa da su.[2]
Ƙungiyar ta shahara bayan wallafa biyon wakarsu a YouTube mai suna "Rozy / Donbass", bisa ga maganan Shakespeare's Sonnet 35 da waƙoƙin jama'a na kasar Ukraine. [3] [4] Hakanan sananne daga cikin bidiyo shine wasan da suka yi na kai tsaye akan Maidan Nezalezhnosti a Kyiv a lokacin zanga-zangar farko ta Euromaidan a cikin Disamban 2013. [5]
Wakoki
gyara sashe- Idan (2016)
- Jirgin sama (2019)
- Make Up (2021)
Manazarta
gyara sashe- ↑ Борис Барабанов Украина на все голоса. Dakh Daughters спели в «Гоголь-центре» Коммерсантъ No. 50 от 26.03.2014.
- ↑ Cultural focus: UKRAINE Archived 2014-04-13 at the Wayback Machine EaP Culture Programme Website
- ↑ Rozy / Donbass
- ↑ Елена Акимова Украинки взорвали YouTube песней «Фантастиш Донбас» Комсомольская правда, 8 августа 2013
- ↑ Hannusya