Kungiyar ‘yan tawayen Moro ta MNLF wato Moro National Liberation Front (MNLF: kungiya ce ta dan tawaye ta ƙasar Philippines wacce aka kafa a Shekarar 1972.[1][2][3] gungiyar MNLF tana gwagwarmaya da gwamnatin Philippines don neman ‘ yancin yankin Bangsamoro. A cikin shekarun da suka gabata an yi kokari da yawa don cimma zaman lafiya tsakanin MNLF da gwamnati. A cikin 1976 kungiyar Hadin gwiwar Musulunci ta shirya yarjejeniya amma hakan ya faskara. A shekarar 1986 Shugaba Corazon Aquino ya sadu da Misuari, kuma a shekarar 1989 aka baiwa yankin matakin cin gashin kai. Shugaba Fidel Ramos ya shirya yarjejeniyar zaman lafiya a 1996 wanda ya ba da damar a zabi Misuari a matsayin gwamnan yankin. Misuari ya jagoranci wani tawaye na adawa da gwamnatin tarayya a 2001, amma hakan ya faskara kuma aka tura shi kurkuku. MNLF ya ce yankin Bangsamoro Land ya game Sulu, Mindanao, Palawan da Sabah (a Malaysia ). MNLF memba ne gungiyar Hadin Kan Islama .

Ƙungiyar Tawaye ta Moro
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa

mnlfnet.com


Tutar MNLF
Gurin moro
kungiyar moro
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Manazarta

gyara sashe
  1. Daniel Cassman (August 14, 2015). "Moro National Liberation Front". Mapping Militant Organizations – Stanford university.
  2. Encyclopædia Britannica Online, s. v. "Moro National Liberation Front (MNLF)", accessed 20 February 2016, http://www.britannica.com/topic/Moro-National-Liberation-Front.
  3. "Focus on the Philippines". Archived from the original on March 5, 2016. Retrieved January 26,2015.

Sauran yanar gizo

gyara sashe