Ƙaranbau
Ƙaranbau cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar ƙwayar cutar varicella-zoster (VZV). Yana iya haifar da ƙaiƙayi, kurji-kamar bororo. Kurjin yakan fara bayyana akan ƙirji, baya, da fuska, sa'annan kuma ya bazu a kan dukkan jiki, yana haifar da bororo tsakanin 250 zuwa 500. Karanbau na iya zama mai tsanani, musamman a jarirai, matasa, manya, mata masu juna biyu, da kuma mutanen da ke da jikin da ke da ƙananan ikon yaƙar ƙwayoyin cuta da cututtuka
Ƙaranbau | |
---|---|
![]() | |
Description (en) ![]() | |
Iri |
viral infectious disease (en) ![]() ![]() ![]() ![]() cuta |
Specialty (en) ![]() |
infectious diseases (en) ![]() pediatrics (en) ![]() |
Sanadi |
Human herpesvirus 3 (en) ![]() |
Symptoms and signs (en) ![]() |
vesicle (en) ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() itch (en) ![]() |
Disease transmission process (en) ![]() |
droplet infection (en) ![]() contact transmission (en) ![]() |
Physical examination (en) ![]() |
physical examination (en) ![]() ![]() ![]() real-time polymerase chain reaction (en) ![]() |
Treatment (en) ![]() | |
Magani |
aciclovir (en) ![]() ![]() ![]() |
Identifier (en) ![]() | |
ICD-10-CM | B01 da B01.9 |
ICD-9-CM | 052 da 052.9 |
ICD-10 | B01 |
DiseasesDB | 29118 |
MedlinePlus | 001592 |
eMedicine | 001592 |
MeSH | D002644 |
Disease Ontology ID | DOID:8659 |
Alamun kamuwa da cutar karanbauGyara
Kurji mai ƙaiƙayi da kamuwa da cutar karanbau ke haifarwa yana bayyana kwanaki 10 zuwa 21 bayan kamuwa da cutar kuma yawanci yana ɗaukar kwanaki 5 zuwa 10. Sauran alamomi, waɗanda za su iya bayyana kwana ɗaya zuwa biyu kafin kurji, sun haɗa da:
- Zazzaɓi
- Rashin ci
- Ciwon kai
- Gajiya ,da jin rashin lafiya, gaba ɗaya (rashin lafiya)
Da zarar kurjin ƙaranbau ya bayyana, yana tafiya da matakai uku: Ƙunƙarar ruwan hoda ko ja (papules), wanda ke fitowa cikin kwanaki da yawa sananan bororo masu cike da ruwa (vesicles), waɗanda ke fitowa nan da kwana ɗaya sannan su karye su zubo bawo da bambaroki, waɗanda ke rufe bororo da suka karye kuma suna ɗaukar ƙarin kwanaki don warkewa[1][2]
Wuraren da ƙaranbau ke fara bayyanaGyara
kurjin na iya fara bayyana akan ƙirji,baya, da fuska, sa'an nan kuma ya bazu a dukkanin jiki, gami da cikin baki, fatar ido, ko yankin al'aura. Yawancin lokaci yana ɗaukar kusan mako guda don duk bororo su zama bambaroki. Sauran alamun da za su iya fara bayyana kwana ɗaya zuwa biyu kafin kurjin sun haɗa da: zazzabi.
ManazartaGyara
- ↑ https://www.google.com/search?q=what+is+chickenpox&oq=what+is+chickenpox&aqs=chrome..69i57j0l3.24020j0j4&client=ms-android-transsiomn-infinix-rev1&sourceid=chrome-mobile&ie=UTF-8
- ↑ https://www.google.com/search?q=chicken+pox+rash+start&oq=chicken+pox+rash+start&aqs=chrome..69i57.2363j0j9&client=ms-android-transsion-infinix-rev1&sourceid=chrome-mobile&ie=UTF-8
Hanyoyin haɗi na wajeGyara
Wikimedia Commons has media related to Ƙaranbau. |
- Ƙaranbau a Curlie
- Prevention of Varicella: Recommendations of the Advisory Committee on Immunization Practices (ACIP), 1996
- Antiviral therapy of varicella-zoster virus infections, 2007
- Epidemiology and Prevention of Vaccine-Preventable Diseases: Varicella, US CDC's "Pink Book"
- Chickenpox at MedlinePlus