Harshen Ika, yare ne na Igboid, wanda aka rarraba shi ƙarƙashin Igboid Nuclear a cikin dangin harshen Yeai.

Yaren Ika
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 ikk
Glottolog ikaa1238[1]

Yaren mutanen Ika ne na jihohin Delta da Edo na kudancin Najeriya amfani da yaren. [2]

Musamman ma, ’yan kabilar Ika suna yankin Arewa maso Yammacin Jihar Delta; amma wasu kamar Igbanke, Inyelen da Ekpon, yanzu haka suna jihar Edo. Al'ummar Ika galibi sun ƙunshi wadannan: Agbor, Owa, Umunede, Mbiri, Abavo, Orogodo, Otolokpo, Igbodo, Ute-Okpu, Ute-Ugbeje, Idumuesah Akumazi, Ekpon, Igbanke, Inyelen, Iru egbede (Jihar Edo). [2]

Sauran al’ummar Ika da aka samu a Jihar Edo sun hada da Owanikeke, Owa-Riuzo Idu, Igbogili, Ute Oheze, Owa Ute, Oheze Ute, Obagie N’Oheze, Oghada, da Ogan da Ute Obagie N’Oheze. A gidan rediyon Delta yanzu akwai labarai cikin yaren Ika. Ikas sun soma rubuta Littafi Mai Tsarki a yarensu, kuma an buga bisharar Markus, Luka, Matta da Yohanna a ,cikin Ika tare da wasu littattafai. Ifeanyi Okowa fitaccen dan Ika ne.

Ika kwatanta phonological

gyara sashe

Takaitacce juxtasion na phonology tsakanin yarukan Ika guda uku daban-daban.

Turanci Yaren Akumuzi (Arewa- Gabas) na Ika Yaren Owa (Arewacin Kudu) na Ika Yaren Agbor (Kudu) na Ika
'tufafi' akwa ekwa ekwa
'takarda' akuwo ekukwo ehhwo
' sandar tauna' atu etu etu
'soso' elu eru eru
'mai dadi' mu mu uswo

Karin bayani

gyara sashe

 

manazarta

gyara sashe
  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Yaren Ika". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
  2. 2.0 2.1 Empty citation (help)
  •  
  •  
  •  
  •  

Samfuri:Languages of Nigeria