Suleiman Nazif

Dan siyasar Najeriya

Sulaiman Mohammed Nazif (An haife shi a ranar goma sha hudu 14 ga watan Afrilun shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in 1970) ya kasance dan siyasan Nijeriya ne kuma an kuma zaɓe shi a matsayin Sanata na mazabar Bauchi ta Arewa a jihar Bauchi, Nijeriya, inda ya ɗauki mukamin a ranar ashirin da tara 29 ga Mayu na shekarar alif dubu biyu da bakwai 2007. An kuma zaɓe shi a ƙarƙashin jami'yyar Action Congress (AC).

Suleiman Nazif
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Bauchi North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Bauchi North
Rayuwa
Haihuwa Jihar Bauchi, 14 ga Afirilu, 1970 (54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Action Congress of Nigeria (en) Fassara

Nazif ya halarci Makarantar Kwalejin Tarayya da ke Bauchi shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da daya zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da ukku (1981-1983), Makarantar Soja ta Najeriya shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas(1983 zuwa 1988) da Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda ya kammala karatunsa a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in 1990 a matsayin Injiniya. Bayan ya hau kujerar sanata a majalisar dattijai, an nada shi ga kwamitocin mata da matasa, Albarkatun ruwa, ma'adanai mai karfi, basussuka na cikin gida da na waje, sufuri na kasa (Mataimakin Shugaban kasa), Magungunan Kwayoyi da Lafiya da Cin Hanci da Sadarwa. An kuma nada shi sakataren watsa labarai na kungiyar dattawan Arewa.[1][2]

Manazarta gyara sashe

  1. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Web.archive.org. Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2020-01-08.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  2. "Nigeria: Yuguda Has Failed to Deliver - Sen Nazif". AllAfrica. Retrieved 2020-01-08.