Niger Tornadoes F.C.

Kungiyar kwallon Kafa ce A Najeriya

Niger Tornadoes Football Club ne a kwallon kafa kulob na tushen a garin Minna, ƙasar Najeriya. A yanzu haka suna wasa a kungiyar tarayyar Najeriya. Filin wasansu shine Bako Kontagora Filin wasa kuma sun buga wasan gida a filin wasa na Confluence a garin Lokoja.

Niger Tornadoes F.C.
Bayanai
Iri ƙungiyar ƙwallon ƙafa
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Minna
Tarihi
Ƙirƙira 1977

Tarihi gyara sashe

A shekarar dubu biyu da biyar 2005 sun kare a karshen rabin gasar Firimiyar Nigeria amma sun kauce daga faduwa da maki uku. Kulob din ya gamu da matsalar kudi, inda ‘yan wasa ke korafin rashin biyansu albashi inda suke bukatar Karin Albashi.

Bayan fara wasa sifili da ukku 0-3 zuwa kakar shekarar dubu biyu da takwas zuwa da tara 2008-09 an kori dukkan masu gudanarwar. Masu maye gurbin shugaban (David Suleiman) da manajan (Danladi Nasidi) suna da matsayi iri daya a kulob din daga shekarar dubu biyu da huɗu zuwa da biyar 2004 - 2005 lokacin da suka karena sha uku 13 da sha huɗu 14 a Premier. A ranar sha biyar 15 ga Nuwamba, ƙungiyar ta ɗauki Justin Tenger a matsayin mai ba da shawara kan fasaha, rawar da yake da ita har zuwa shekarar dubu biyu da huɗu 2004.

Sun fice daga gasar Premier a shekarar dubu biyu da sha biyu 2012 kan banbancin kwallaye bayan sun ci kwallaye talatin da takwas 38 a wasanni talatin da shida 36. Goma sha uku daga cikin kwallayen Sibi Gwar ne ya zira kwallaye a raga. Sun sake cin nasara a shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015 bayan sun ci Kofin Najeriyar na Kasa.

Niger Tornadoes ta sami koma baya zuwa babban rukuni a cikin shekarar dubu biyu da sha biyar 2015. Koci Abdullahi Biffo ne ya jagorance su zuwa ci gaban da suka samu bayan sun lallasa Mighty Jets FC da ci biyu 2 da nema 0.

Niger Tornadoes ce ta zo ta biyu a gasar cin kofin FA ta Najeriya a shekarar dubu biyu da sha bakwai 2017 bayan ta sha kashi a bugun fenariti a hannun Akwa United.

An ci tarar kulob din kudi N1 miliyan a shekarar 2019 saboda matsalar mutane a wasan da suka buga da Bendel Insurance.

Nasarori gyara sashe

  • Kofin FA na Najeriya : 1
2000
  • Rukuni na Biyu na Kasa : 2
1996, 2015

Ayyuka a cikin gasa CAF gyara sashe

  • CAF Cup Winners 'Cup : bayyanuwa 1
2001 - Kwata kusa dana karshe
  • Gasar WAFU Club : fitowa 1
2010 - Kwata kusa dana karshe

Kungiyar yanzu gyara sashe

Kamar yadda na 11 Fabrairu 2019  

No. Pos. Nation Player
1 GK   NGA Ndem Innocent
2   NGA James Martins Iko
3 FW   NGA Anthony Onyebuchi Onyeakazi
4   NGA Moses Ugwu
5 DF   NGA Sunday Akinmoladun
6 DF   NGA Sarki Ismaila
7 MF   NGA Tanko Awwal
8 MF   NGA Adetola Ayo
10 MF   NGA Ahmed Liman
11   GHA Eric Frimpong
13   NGA Peter Abashiya
14 MF   NGA Obinna Jacob
No. Pos. Nation Player
17 DF   NGA Ibrahim Babawo Abubakar
20 FW   NGA Mustapha Jibrin
21 DF   NGA Andrew Ikefe
22 FW   NGA Osondu Jonathan
23 FW   NGA Udeh Clement
27   NGA Atsen Emmanuel
28   NGA Iorliam Gwaza
30 GK   NGA Mustapha Salihu Aliko
32   NGA Mohammed Aliyu
33   NGA Wakili Musa Abdullahi
34   NGA Mushinu Attairu
35 MF   NGA Abiodun Afolabi
36   NGA Mohammed Abubakar
38   NGA Bashar Usman

Manazarta gyara sashe