Major General faruok yahaya

Sake dubawa tun a 23:42, 30 ga Yuli, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966. Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990. Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka: Laftana - ranar 27 ga Satumba 1990 Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba 1994 Manjo - ranar 27 ga watan Satumba 1998. Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003. Kanar -...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)

An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966. Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990. Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka: Laftana - ranar 27 ga Satumba 1990 Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba 1994 Manjo - ranar 27 ga watan Satumba 1998. Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003. Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2008 Birgediya Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2013 Manjo Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2017. Sabon babban hafsan sojin kasan na Najeriya ya yi karatun digirinsa na farko a fannin Tarihi sannan ya yi digiri na biyu wato Masters a kan harkokin siyasar kasashen duniya da difilomasiyya. Ya rike mukamai daban-daban ciki har da mataimakin sakataren rundunar soji da kuma sakataren na rundunar soji a hedikwatar sojin kasa. Mukamin da ya rike na karshe kafin naɗin nasa shi na jagorantar yaƙi da Boko Haram karkashin rundunar Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya. Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko wato General Officer Commanding (GOC) 1 Division. Kafin nadinsa a mukamin General Officer Commanding 1 Division, Manjo Janar Yahaya ya jagoranci runduna ta 4 da ke hedikwatar rundunar sojin Najeriya. Kazalika ya rike mukamin Kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, a jihar Borno. A shekarar 2019, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jagoranci rundunar Operation CLEAN SWEEP wadda ta fatattaki 'yan bindigar da ke dajin Kuduru a Birnin Gwari na jihar Kaduna. . Yanzu shine babban Hafsan Sojojin Nigeria

. < https://www.bbc.com/hausa/labarai-57273207\>

https://www.bbc.com/hausa/labarai-57273207×> <