1 Asalin Yesu Almasihu (Luka 3.23-38) 1Littafin asalin Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan. 2Ibraham ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da 'yan'uwansa, 3Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (mahaifiyarsu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram, 4Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya Kuma haifi Salmon, 5Salmon ya haifi Bo'aza (mahaifiyarsa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse, 6Yesse ya haifi sarki Dawuda. Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda mahaifiyarsa dā matar Uriya ce), 7Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, 8Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya, 9Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya, 10Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya. 11Yosiya ya haifi Yekoniya da 'yan'uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila. 12Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel, 13Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro, 14Azuro ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu, 15Aliyudu ya haifi Ele'azara, Ele'azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu, 16Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu. 17Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu. Haihuwar Yesu Almasihu (Luka 2.1-7) 18Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki. 19Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama'a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce. 20Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, 23“Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, Za a kuma sa masa suna Immanuwel.” (Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah yana tare da mu.) 24Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala'ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa, 25amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.

Matiyu
Asali
Mawallafi Matthew the Apostle (en) Fassara
Asalin suna εὐαγγέλιον κατὰ Μαθθαῖον da Evangelium nach Matthäus
Characteristics
Genre (en) Fassara Gospel (en) Fassara
Description
Ɓangaren Sabon Alkawari
canonical Gospels (en) Fassara
Tetraevangelion (en) Fassara

Manazarta gyara sashe