Lawrence oluwawemimo arokodare an haife shi ne a rana ta shabiyar ga watan maris shekara ta dubu 1938. Injiniyan farar hula ne na Najeriya, ya kafa kamfanin Etteh Aro da Abokan Hulda, Babban Kamfanin Bada Shawarwari na Injiniyoyin Jama'a a Najeriya. Ya kasance dan asalin Ijero Ekiti a jihar Ekiti, kudu maso yammacin Najeriya. Ya fara aikinsa a Ove Arup da Partners a 1964 kuma ya yi aiki a can har zuwa 1970 lokacin da ya fara aikin sirri tare da abokin karatunsa na digiri. Falsafarsa ta haɓaka ƙwararrun ƴan asalin ƙasa a cikin aikin Injiniya na farar hula, ya jagoranci kamfanin da ya kafa don ɗaukar nauyin ma'aikatan injiniyoyi sama da 55 don karatun digiri na biyu a wajen Najeriya. Ya shiga cikin tsarawa da kula da ayyukan Injiniya da dama a lokacin rayuwarsa.[1]

Manazarta gyara sashe

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Lawrence_Oluwawemimo_Arokodare