☘️☘️☘️

LADUBBAN KWANCIYA BACCI

☘️ Ana son yin alwala kafin kwanciyar bacci

Al-Baraa Bn Aazib رضى الله عنه ya ce: "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce da ni, idan zaka kwanta barci ka yi alwala kamar yadda ka ke yin alwala idan zaka yi Salla, ka kwanta a bangarenka na dama, sannan ka ce,

اللهم أسلمت نفسي إليك وفوضت امري اليك والجات ظهري إليك رهبة ورغبة إليك لا ملجأ ولا منحا منك الا اليك، آمنت بكتابك الذي أنزلت وبنبيك الذي ارسلت

Idan ka mutu cikin wannan dare, ka mutu akan fidra. Ka sanya su karshen abin da zaka fada". Bukhari:6311, Muslim

☘️ Huzaifa رضى الله عنه ya ce: "Idan Annabi صلى الله عليه وسلم zai kwanta bacci da daddare yana sanya hannunsa karkashin kumatunsa, sai ya ce,

اللهم باسمك اموت وأحيا".

         Bukhari, Muslim

☘️ Ban da kwanciya rub da ciki

Ya'iish Bn Dhikhfa Al Ghifary رضى الله عنه ya ce, baba na ya fada cewa: lokacin da nake kwance na yi rub da ciki a masallaci, sai wani mutum yake zunguri na da kafarsa ya ce: "Lallai wannan irin kwanciya Allah سبحانه وتعالى baya son ta". Ya ce, sai na duba mai maganar sai na ga ashe Annabi صلى الله عليه وسلم ne. Abu Dàwud

☘️ Karanta Qul Huwal Lahu Ahad, Qul a'uzu bi Rabbil falaq, Qul a'uzu bi Rabbin nàs

Nana Aisha رضى الله عنها ta ce: "Cikin kowane dare idan Annabi صلى الله عليه وسلم ya je kwanciya sai ya hada hannayensa ya karanta  قل هو الله احد، da قل اعوذ برب الفلق، da قل اعوذ برب الناس.

Sai ya shafe dukkan jikinsa gwargwado. Yana fara shafa kansa da fuskarsa, sannan sauran jikinsa. Yana yin haka sau uku". Bukhari Muslim

☘️ Karanta Àmanar Rasuul

Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce : "Wanda ya karanta ayoyin karshe na cikin suratul Baqara "آمن الرسول" da daddare sun isar masa". Bukhari Muslim

Ma'ana, kariya ce a gare shi daga wani sharri.

☘️ Ana son yin Tasbihi da Tahmidi da Hamdala

Sayyidna Ali رضى الله عنه ya ce: "Nana Fadima رضى الله عنها ta kai kukanta wajen Annabi صلى الله عليه وسلم dongane da wahala da take sha wajen nika, ya taimaka mata da yar aiki. Lokacin da ta je bata same shi ba sai ta gaya wa Nana Aisha رضى الله عنها abin da yake tafe da ita. Da Annabi صلى الله عليه وسلم ya dawo sai Nana Aisha رضى الله عنها ta ba shi labarin zuwan Nana Fadima. Sayyidna Ali رضى الله عنه ya ce, sai Annabi صلى الله عليه وسلم ya zo mana bayan mun riga mun kwanta. Sai na yunkura zan tashi sai ya ce, yi kwanciyarka. Sai ya zauna a tsakanin mu, har sai da na ji sanyin dugaduginsa a kirjina. Sai ya ce ba na sanar da ku abin da ya fi alheri a kan abin da kuka tambaya ba? Idan kun je shimfidarku  ku yi Tasbihi (subhànallah) 33, Alhamdulillah 33, Allahu Akbar 34. Wannan ya fi muku alheri da yar aiki". Bukhari

Ibn Taimiyya رحمه الله تعالى  ya ce, Wanda ya dawwama a kan yin wannan zikiri lokacin da ya zo bacci ba zai dinga jin wahalar aiki ba.

والله تعالى اعلم

أسأل الله العظيم أن ينفعنا واياكم

                 ☘️☘️☘️