✺✺ KYAUTATA ALWALA ✺✺

.

Kyautata alwala abune mai matuqar muhimmanci ga rayuwar bawa, musamman idan muka yi duba zuwa ga irin darajar da ma'abota kyautata alwala zasu samu na sakamako kamar yadda yazo daga Hadith:

.

✿ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda yayi alwala ya kyautata, laifukansa suna fita daga jikinsa har su fita ta qarqashin faratunsa."

.

[Sahih Muslim 245]

.

✿ Daga Na'im binul mujmir daga Abu-hurairah (RA) daga Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa Yace: "Lallai al'ummata za'a qirasu a ranar alqiyama, suna masu alamu na haske da alamu a qafafuwansu na alwala, duk wanda yake da daman tsawaita haskensa sai ya aikata."

.

✿ Acikin lafazin Muslim: Naga Abu-hurairah na alwala sai ya wanke fuskarsa da hannuwansa, har yakusan kai kafad'arsa, sannan ya wanke qafafuwansa har ya d'ago tsintsiyar qafarsa, sannan Yace: Naji Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: "Lallai al'ummata za a qirasu ranar alqiyama suna masu alamu na hasken fuska da hannuwa da alamu a qafafuwansu na alwala, wanda ya samu iko ya tsawaita (guraben) haskensa da shaidarsa sai ya aikata."

.

✿ A wani lafazin na Muslim kuma: Naji Khalili (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: "Ado/qyalqyali na kaiwa ga mumini tsawon yanda alwalarsa takai."

.

→ Wannan hadisan suna kwad'aitar mana da falalar cika guraben alwala ne yadda zasu kasance ranar alqiyama cikin haske kamar wata, kama daga fuska hannu qafa da kai da dai sauransu shine Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) ke kwad'aitar damu tsawaita wannan haske ajikin mu.

.

◉ ABUN LURA: Yadda zamu yi shine idan mun wanke hannun mu zuwa idon hannu to ana so mu ringa qara koda inci 2 ne, haka ma qafa ya zamo mun d'ago saman qaurinmu. Wannan kwad'aitarwa ne ba ace maka dole ba, domin ko wanki d'ad'd'aya kayi kuma ka kyautata alwalarka to ta inganta inshaa ALLAH.

.

★KYAUTATA ALWALA A LOKACIN SANYI:

.

Sau da yawa mutane suna wasa da wannan dama, musamman a lokacin sanyi, sai su ringa yin alwala shafa-shafa irin alwalar 'Yan shi'a, domin nasha ganin 'Yan shi'a suna alwala basa wanke duka guraben alwala, to haka wasu suke komawa yi a lokacin sanyi. Masoyin mu Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kwad'aitar damu game da kyautata alwala a lokacin sanyi kamar yadda yazo a hadith:

.

✿ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: "Shin ba zan shiryar da ku abinda (idan kuka aikata shi) ALLAH zai share muku kurakuran ku kuma ya d'aukaka darajojin ku? Sai (Sahabbai) suka ce: Eh Ya Rasulullah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Sai Yace: "Kyautata alwala a lokacin qi (misali: lokacin sanyi), da yawaita tattaki zuwa masallaci da kuma jiran Sallah bayan Sallah, wancanenku shine rabad'i, wancanenku shine ribad'i (wannan shine juriya kuma abunda ake kwad'ayi)."

.

[Muslim da Ahmad ne suka ruwaito shi, daga Abu Hurairah - Sahihul Jami'i 2,618]

.

Don haka 'Yan uwa muyi qoqari wajen ganin mun kiyaye kyautata alwalar mu, kada mu biyewa lokacin sanyi mu ringa alwala irinta 'Yan shi'a.

.

ALLAH Ya bamu ikon kyautatawa (Ameen)