Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Duniya

Kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya kungiya ce ta agaji da gudanar da ayyukan jin kai mai zaman kanta wato ba ta gwamnati ba ce, helkwatarta kuwa tana a birnin Geneva na kasar habasha ne.

Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Duniya

Neutrality, Independence, Impartiality, Humanity, Universality, Unity, Voluntary Service
Bayanai
Gajeren suna ICRC da CICR
Iri international non-governmental organization (en) Fassara
Ƙasa Switzerland
Aiki
Mamba na Memoriav (en) Fassara da DLM Forum (en) Fassara
Bangare na Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta kasa da kasa
Ma'aikata 25 (2016)
Mulki
Shugaba Mirjana Spoljaric Egger (en) Fassara
Shugaba Robert Mardini (en) Fassara
Hedkwata Geneva (en) Fassara
Tsari a hukumance association (en) Fassara
Mamallaki Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta kasa da kasa
Financial data
Budget (en) Fassara 1,900,000,000 Fr (2019)
Tarihi
Ƙirƙira 17 ga Faburairu, 1863
Wanda ya samar
Awards received

icrc.org


Comité international de la croix rouge
Henri Dunant (1828-1919)

Tarihi gyara sashe

Duk da cewa an kafa kungiyar agaji ta Red Cross din ne 1863 to amma tunanin kafa kungiyar ya faro ne a shekarar 1859 lokacin da dan kasuwan nan kuma mai gudanar da ayyukan jin kai da zamantakewa dan kasar Switzerland wato Jean Henry Dunant wanda daga baya aka fi sani da Henry Dunant, ya irin ababe masu tada hankali da suka faru a lokacin yakin Solferino a kasar Italiya na yanzu, inda dubban mutane suka mutu wasu da dama kuma suka sami raunuka, a bangare guda kuma wadanda suka sami raunukan sun sami samun magani da kulawar da suke bukata. To bayan dawowarsa gida Geneva ne ya yi kira da a kafa kungiyar agaji don ba da taimako ga wadanda suka jikkata a fagen yaki. Hakan ne ya sanya aka kafa kwamitin Red Cross a shekarar 1863.

To amma a wancan lokacin kusan kasashe daban-daban suna da nasu kungiyar ta Red Cross ko kuma ta agaji, to amma an kafa asalin kungiyar Red Cross din ta kasa da kasa ne a shekarar 1919 bayan yakin duniya na farko lokacin da shugaban kwamitin Red Cross na Amurka a lokacin yaki Henry Davison ya ba da shawarar kafa wata hadaddiyar kungiya ta kungiyoyin Red Cross na kasashe daban daban don jagorantara kan ayyukan ba da agaji a duk fadin duniya. A farkon shekarar 1919, an kira taron kasa da kasa kan harkokin kiwon lafiya a birnin Cannes na kasar Faransa. A yayin wannan taron an tsai da shawarar cewa dole ne a kafa hadaddiyar kungiya ta kungiyoyin Red Cross ta kasashe daban daban gaba daya don kara inganta nasarorin da kungiyoyin agaji na Red Cross na kasashe daban daban suka cimma, an dai ba wa wannan kungiya sunan League of Red Cross Societies. Daga baya, saboda shigowar kungiyoyin Red Crescent na kasashen Larabawa da kuma karuwarsu, kungiyar Red Cross ta kira babban taro na uku a watan Oktoba na shekarar 1983, inda aka yanke shawarar sake sunan kungiyar zuwa International Red Cross and Red Crescent Societies (kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya).

Ko shakka babu kafa wannan kungiyar ta Red Cross da Red Crescent tana da alaka da lamari na addini. Saboda kuwa kamar yadda muka ce sakamakon shigowar kasashen musulmi cikin wannan lamari na ba da agaji sosai ya sanya wasu suna ganin bai kamata su ci gaba da amfani da cross ba wanda a bangare guda yana a matsayin alama ce ta mabiya addinin kirista wato alamar da suke amfani da ita don nuna giciye Annabi Isa al-Masihu (a.s) da aka yi don haka wasu suka fara tunanin su ma musulmi su kirkiro wata alamar ta su a wannan bangaren. To da yake ana amfani da alama ta wata a matsayin abin da ke nuni da Musulunci wanda hatta ko a hasumiyar masallatai a kan sa hakan don haka sai suka yi amfani da wannan alama ta wata a matsayin alamarsu. Don haka ne alamar wannan kungiya ta zamanto cross da kuma alamar wata (ko kuma crescent a turance.

An amince da wannan alama ta crescent ne kuwa a hukumance a shekarar 1929 kuma ya zuwa yanzu kimanin kasashe 33 ne suka amince da hakan. Duk da cewa an fara amfani da wannan alama ce tun a shekarar 1877-1878 lokacin rikici da yakin da aka yi tsakanin kasashen Rasha da Turkiyya.

Manufar ita ma wannan kungiya ta Red Cross da Red Crescent ita ce ba da agaji da jin kai ga wadanda suka sami raunuka a lokacin yaki har ila yau da kuma batun kiyaye sulhu da zaman lafiya.

Wani lamari kuma da ya ke da kyau a fahimta shi ne cewa kasashe biyar ne ake daukansu a matsayin wadanda suka kafa ita wannan kungiyar ta Red Cross, su ne kuwa: Birtaniya, Faransa, Italiya, Japan da kuma Amurka. To sai dai daga baya sun ta karuwa lokacin da kungiyoyin red cross da na red crescent na kasashe daban-daban suka ta shigowa cikin uwar kungiya inda ya zuwa yanzu akwai sama da kasashe 180 a cikin kungiyar. A takaice dai ana iya cewa kusan dukkanin kasashen duniya suna da ko dai k kungiyar agaji ta Red Cross ko kuma ta Red Crescent

Ayyukan kungiyar gyara sashe

Ma`aikatan kungiyar gyara sashe

Manazarta gyara sashe