Khalil Nur Khalil shi ne mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin tattalin arziki, Dikko Umaru Radda. Ya kasance tsohon babban sakataren hukumar bunkasa zuba jari ta Kaduna (KADIPA) da aka nada a watan Oktoban 2021, karkashin Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna.[1]

Sannan kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar tattalin arzikin jihar Katsina, tare da wasu fitattun ‘yan majalisar ministoci.


An haife shi a ranar 18 ga Nuwamba, 1992 a jihar Kaduna inda ya yi karatun firamare a makarantar Kaduna International School, ya ci gaba da samun IGCSE a British International School, Victoria Island, Legas da GCE Advanced Level (A-Levels). Yin Karatu a Glenalmond College a Perth, Scotland.[1]

  1. 1.0 1.1 https://businessday.ng/opinion/article/khalil-nur-khalil-new-kid-on-the-block-of-nigerias-public-service/