Khadijeh Saqafi (an haife ta a shekara ta 1916.- 21 ga watan Maris din Shekarar 2009) ( Persian , wanda akewa laƙabi da Qudus din Iran ita ce matar Ruhollah Khomeini, shugaban juyin juya halin Iran na shekara ta 1979.

Khadijeh Saqafi
Rayuwa
Haihuwa Tehran
ƙasa Iran
Mazauni Tehran
Mutuwa Tehran, 21 ga Maris, 2009
Makwanci Behesht-e Zahra (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Khomeini  3 ga Yuni, 1989)
Yara
Karatu
Harsuna Farisawa
Sana'a
Sana'a revolutionary (en) Fassara
Imani
Addini Shi'a

Rayuwar farko gyara sashe

Saqafi ɗiya ce ga Haj Mirza Mohammad Saqafi Tehrani babban malami mai daraja. Haj Mirza Mohammad Saqafi jikan Agha Mirza Abolghassem Kalantar, magajin garin Tehran a ƙarƙashin Qajars a tsakiyar karni na sha tara.

Saqafi ya auri Ruhollah Khomeini a shekarar 1929, lokacin tana da shekaru 13 Ta haifi yara bakwai tare da Khomeini yayin rayuwarta, kodayake biyar kawai suka rayu tun suna yara. Danta, Mostafa, ya rasu a Iraki a shekarar 1977, yayin da na biyu, Ahmad, ya mutu sakamakon bugun zuciya a 1995 yana da shekara 49.

An bayyana Saqafi, wacce galibi ba ta fita daga idanun jama'ar Iran ba, an bayyana ta a matsayin babbar mai goyon bayan adawar mijinta ga Shah na Iran. Tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hashemi Rafsanjani, ya ambaci Saqafi a matsayin "makusanciya kuma mafi hakuri" ga mijinta.

File:Khadijeh Saqafi.jpg

Mutuwa gyara sashe

Saqafi ta rasu a ranar 21 ga Maris 2009, a Tehran bayan doguwar rashin lafiya tana da shekaru 93. Dubun-dubatar mutane ne suka halarci jana’izarta, ciki har da Jagoran Iran Ali Khamenei da na lokacin Shugaba Mahmud Ahmadinejad. An binne Saqafi kusa da mijinta a kabarinsa da ke Behesht-e Zahra. Ta bar ƴaƴa mata uku, Zahra, Sadiqeh, da Farideh.  

Manazarta gyara sashe