Kabarin Tafawa Balewa dai shi ne wurin da aka binne Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Bauchi, cikin Jihar Bauchi dake tarayyar Najeriya wanda shi kaɗai ne ya taɓa yin wannan muƙami na Firimiyan Najeriya. [1]

Babban Kofar Kabarin Abubakar Tafawa Balewa
Kabarin Tafawa Balewa
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Bauchi

Tarihi gyara sashe

A lokacin juyin mulkin Najeriya a shekarar 1966, an yi garkuwa da Abubakar Tafawa Balewa, firaministan Najeriya, inda aka tsinci gawarsa a bakin titi kwanaki shida bayan sace shi. [2] Daga nan aka binne shi a Bauchi inda aka haife shi. A ranar 29 ga watan Agustan shekarar 1979 ne aka ayyana kabarinsa a matsayin wani abin tarihi a fadin ƙasar Najeriya, wanda hadimin soja na jihar, Birgediya Garba Duba ya yi.[3][4]

 
Allon Kabarin Abubakar Tafawa Balewa

An fara gina wannan abin tarihin da kuma gine-ginen da ke kewaye da kabarin a shekara ta 1977 kuma an ba da izini a watan Yuli 1979.[5]

 
Kabarin Sir Abubakar Tafawa Balewa

Manazarta gyara sashe

  1. Times, Lloyd Garrison Special To the New York (1966-01-23). "NIGERIA DISCLOSES DEATH OF BALEWA; Kidnapped Prime Minister's Body Found on Roadside-- Mourning Is Decreed Nigeria Discloses the Death of Balewa". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2022-04-06.
  2. "Tafawa Balewa: 1912 to 1966". The Nation Newspaper (in Turanci). 2016-01-14. Retrieved 2022-04-06.
  3. "SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA TOMB MONUMENT". Visit Nigeria Now (in Turanci). Retrieved 2022-04-08.[permanent dead link]
  4. "'He Died And Left Office Without Having Mansions,' Bauchi Remembers Tafawa Balewa | Channels Television". www.channelstv.com. Retrieved 2022-04-08.
  5. "Gidan Beminister, Mapi Hall, others for national monuments". Daily Trust (in Turanci). 2017-12-02. Retrieved 2022-04-06.