KA AURI MAI ADDINI;

-

"Idan ka tashi yin aure kada kabi ƙyale-ƙyalen kyawun fuska, ko dukiya ko kuma nasaba, domin duk waɗannan anan duniya kaɗai suke da ta'asiri, kuma a duniyar ma bai zama lallai suyi dogon zango ba"

-

MANZON ALLAH ﷺ, YACE:

Ana auren mace ne domin abubuwa huɗu:

-

❤️DOMIN DUKIYARTA.

❤️DOMIN NASABARTA.

❤️DOMIN KYAWUNTA.

❤️DOMIN ADDININTA.

-

"To amma ka zaɓi mai addini, (in ba haka ba) za kayi asara"

Sahih Al-Bukhari (5090)

-

"Lallai duk waɗannan abubuwan suna sawa aso mutum, amma aso wanda yakeda addini shine yafi dacewa"

-

"Kuma duk wanda ya saɓawa shawarar  Manzon Allah ﷺ, to lallai haƙiƙa zaiyi da-nasani anan gaba, koda kuwa farkon lamarin nashi yayi masa kyawu"