KAKUMI Wannan kauye ne a cikin karamar hukumar bakori a jahar katsina,

Garin na Kakumi yana makotaka da Kananan hukumomi kamar haka; daga gabas yana iyaka da Kankara, daga Yamma yana iyaka da Faskari.

MUTANE NAWANE A GARIN KAKUMI?

Garin Kakumi yanada adadin mutane a kalla Dubu 40,000 da doriya.

MENENE SANA'AR MUTANEN GARIN KAKUMI?

Sana'ar mutanen garin wacce sukafi amanna da ita itace noma da kiyo.

YAUSHE DAMINA TAKE KAMAWA A GARIN KAKUMI?

Ruwan damina yana farawa ne daga watan May har zuwa watan November.

SUWA NENE SUKA FARA ZAMA A KAKUMI?

Garin na Kakumi yanada da tarihi Mai tsaho, Wanda ya samo asali ne tunda daga mutanen dauri, wajajen shekara ta 1907, tun kafin wannan zuwan turawa Nigeria akwai hujjojin da suka tabbatar da cewa akwai mazauna a wannan yanki da ake kira Kakumi a yanzu. Kenan zamu iya cewa garin Kakumi ya Dade da kafuwa, duk da cewa takamaimai bazaace ga lokacin garin ya kafu ba.

Edited by Badaru Shehu AKA Badarancy.