Jika Dauda Halliru

Sanata a Najeriya

An haifi Jika Dauda Halliru a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da shida 1976 a jihar Bauchi, Nigeria. Dan kasuwa ne kuma dan siyasa. Ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi kuma a yanzu haka dan majalisar dattawa ne mai wakiltar Bauchi ta tsakiya. An fi saninsa da Dokagi.[1][2]

Jika Dauda Halliru
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Bauchi Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Bauchi Central
Rayuwa
Cikakken suna Jika Dauda Haliru
Haihuwa 1976 (47/48 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Ilimi gyara sashe

Ya tafi Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna, Jihar Kaduna ya kammala a shekara ta alif ɗari tara da casa'in da tara 1999. Daga nan ya koma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna domin yin karatun Injiniya, kuma ya kammala a shekara ta 2003.

Harkar siyasa gyara sashe

An zabi Jika a matsayin wakilin mazabar Darazo da Ganjuwa a majalisar wakilai ta tarayya kuma ya yi zango biyu a matsayin wakili, na farko tsakanin shekara ta 2007 da shekara ta 2011 da kuma na biyu tsakanin shekara ta 2011 da shekara ta 2015. Sannan a zaben shekara ta 2019 an zabe shi sanata bauchi ta tsakiya karkashin tutar APC.

Rayuwar mutum gyara sashe

Jika musulmi ne. Yayi aure da yara.

Manazarta gyara sashe

 

  1. Babah, Chinedu (2017-10-04). "JIKA, Hon Dauda Haliru". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2020-02-20.
  2. "Hon. Jika Haliru biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2020-02-20.