Hajiya (Dr.) Fatima Lami Usman Kurfi

Hajiya (Dr.) Fatima Lami Usman Kurfi shaharriyar mai aiwatar da ayyukan jin-qai a Kurfi ta Jihar Katsina ce. Wadda Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria ta ba digirin girmamawa a ranar 28 ga watan Janairu, 2023 a wajen taron yaye dalibai karo na 42 da Jami'ar ta gudanar.

Hajiya (Dr.) Fatima Lami Usman Kurfi 'yar shekaru 86 a duniya a halin yanzu ta kammala digirinta a Jami'ar Alqlam dake Katsina a shekarar 2015 tana da shekaru 78 a duniya.

Hajiya (Dr.) Kurfi ta yi aiki da Kungiyoyin Jin-qai na kasa da kasa daban-daban. Sannan kuma ta samar da makarantu. Ta kuma dauki dawainiyar dalibai da dama, musamman ma mata domin samun gudanar da karatu mai zurfi.[1] Archived 2023-09-06 at the Wayback Machine