Hairat Abdullahi wasu sunfi sanina da Khairat Abdullahi (An haife ni a shekara ta alif 1998) a cikin garin Kaduna, Najeriya. Fitacciyar mawakiyar Hausa ce ta Soyayya,Siyasa da kuma Sarauta a masana'antar ta Kannywood.

Wadda take zamaninta tun farkon lokacin data bayyana a masana'antar Kannywood a shekara 2013, Ta fara samun nasara daga wakokin gamayya da tayi da mawaka kamar haka:

Umar M Shareef, Abdul D-One, Umar Mb da Muhammad meleri, bayan haka Hairat tauraruwarta taketa haskawa haryanzu a wannan masana'antar.

Khairat tayi wakoki da matasan mawaka kuma haka ya taimaka musu wajan samun nasu gurbi a masana'antar. Wakoki kamar haka: Zo mu sasanta,Labarina, Dillin Dillin da sauransu.

A shekara ta 2023 ta saki karamun kundinta wata (Ep) me dauke da wakoki 5 wato (Da Raina Ep) Wanda tasamu nasara ba karamar ba a kansa wadda haryanzu wakokin suna tashe a gidajen radio,Tv da dukkan kafafen sada zumunta na duniya.






[1]

[1]

  1. https://aminiya.ng/mawakan-kannywood-mata-da-ba-a-san-su-ba/