HUKUNCIN AURE:

An sunnanta wa wanda yake da yawan sha’awa kuma ba ya tsoron afkawa zina. An wajabtawa wanda yake tsoranta. An halastawa wanda baida sha’awa, kamar mai guntun gaba da babba, kuma an haramta aure a garin da kuke yaki da su ba tare da wata lalura ba.

Sigar Aure.

Ana daura aure da ko wanne irin lafazi wanda yake nuni da shi, da kuma kowanne yare sai a ce: Na aurar ko ya ce : Na karbi wannan auren, ko na yarda. Kuma an so a yi shi da harshen Larabci, wanda kuma ba su san shi ba sai ya yi da yaren sa.

Rukunan Aure:

Aure nada rukune biyu:

1. Bayarwa: shi ne lafazin da waliyli zai furta, ko wanda ya wakilce shi da lafazin aure ko na aurar, domin sune lafuza wanda Alkur’ani ya zo da su, Allah Ta’ala ya ce:

﴿ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَاءِْ٣﴾

Ma’ana: “Ku auri abin da ya yi maku dadi daga mata”. …….(Nisai:3).

2. Karba:- shi ne lafazin da miji zai furuta ko wakilin sa da fadin cewa: Na karba ko na yarda. Kuma ya kasance bayarwa ya riga lafazin karba zuwa sai dai inda wani abu da ka lura da shi.

SHARUDAN AURE HUDU NE.

1. Tabbatar ma’aurata biyu tukunna.

2. Yardar ma’aurata, ba ya halatta a tilasta daya daga cikin su akan sai ya auri dayan. Za’a nemi izinin budurwa da bazawara, izinin budurwa shi ne shiru, bazawara kuma Magana, ba’a shardanta hakan bag a mahaukaci ko maimatsalar magana.

3. A samu waliyyi, an yi sharadi da ya kasance na miji ‘da, baligi, mai hankali mai lura, adali. An shardanta addini ya zamo daya, baban mace shi ya fi cancantar ya aurar da ita, sannan wanda aka yi wa wasiyya, sannan Kakanata mahaifin uba, har sama. Sannan ‘dan ta koda lissafin ya yi kasa (jika, jikan-jika…), sannan ‘dan’uwanta uwa-daya-uba daya, sannan dan’uwanta uba-daya, sannan ‘ya’yansu a hakan, sannan baffa (kanin baba ko uwan shi) na ‘uwa-daya-uba-daya, sannan baffa na uba-daya, sannan ‘ya’yan su, sannan wanda ya fi kusa a dangi, sannan sarki.

3. Shaidu, Aure ba ya inganta sai da shaidu biyu, adilai, maza, wadanda hukunce hukunce suka hau kansu.

4. Samun ma’aurata da babu wani da zai hana auran.

Abunda aka sunnanta da wanda aka haramta a aure.

- An sunnanta auren mata daya idan mutum ya ji tsoron adalci, addini, wacce ba kabila guda ba, budurwa, hai huwa, kyakkyawa.

- Ya halatta ga wanda ke neman aure ya yi dubi matar da zai aura ba tare da ta bude al’urar ta ba, da kuma abun da zai jawo shi zuwa ga auranta, ba tare da sun kebanta ba, haka ma mace ta kalli wanda za ta aura.

- Idan bai samu damar ganinta ba sai ya aiki wata matar da za ta yi mu’amala da ita don ta zo ta siffanta masa ita, ya haramta ga namiji ya yi neman aure kan neman dan’uwa sa har sai ya bari ko ya yi masa izini.

- An halatta bayyanannen bayani ko jurwaye mekama da wanka a wajan neman mace wadda aka sake ta saki daya ko biyu wanda ke nisantar da ita ga mijinta wanda ma bai kai ukun ba.

- Ya haramta a nemi auran matar da aka saketa sakin da za’a iya kome to ya haramta a bayyana nemanta ko ayi jurwaye mai kama da wanka, muddin tana cikin iddarta.

- An sunnanta daura aure aure ranar jumu’ah da yamma, domin akwai wani lokaci mai albarka wanda ake karbar addu’a, kuma an sunnanta a yi a masallaci in https://islamhouse.com/read/ha/fikhu-a-sawwake-2778721#t79