GARIN MAYANCI
Garin Mayanci ya kafu a shekara ta 1825, ƙarƙashin jagorancin Na'ali Damamisau da jama'arsa, waɗanda suka fito daga wani ƙauye da ake kira Birnin Fulani da ke Maru. Sun ya da zango a wani wuri da ake kira Garagin Yahaya da ke yankin ƙaramar hukumar Talatar Mafara ta yanzu tare da dabbobinsu, daga baya suka koma Mayanci a shekarar 1825[9]
Kafin kafuwar Mayanci ana kiranta da suna "Mayauta" wato wurin yini, ita wannan Mayautar wuri ne da ake kiwon dabbobi, kuma akwai namun daji a wannan wurin da sauransu. Bayan Na'ali Damamisau da jama'arsa sun dawo garin Mayauta (Mayanci), da yake lokacin yaƙe-yaƙe ne na kare kai da iyali, Na'ali ya yi nasarar kashe zakin da ya addabe su wanda an ce da zakin ya yi wata ƙara lokacin mutuwarsa har mutanen Murai sai da suka ji ƙararsa. Bayan sun sami kwanciyar hankali ne suka canza wa wannan gari suna daga Mayauta zuwa mayanci.[10]
Kafuwar garin Mayanci daga 1825 zuwa yanzu an yi sarakuna goma sha bakwai, ga su kamar haka tare da shekarun da suka yi mulki:
1. Na'ali Damamisau 1825-1847
2. Ba'atsoro Buba Ɗan Na'ali 1847-1866
3. S/Kanoma Zaki 1866-1882
4. Rafi Bawa 1882-1890
5. Doshiro Gajere mai dubara 1890-1904
6. Muhammad Bube 1904-1916
7. Ɓaidu kutsa Gatan Mani 1916-1924
8. Ɓawo zarumi 1924-1936
9. Dodo El-Umar 1936-1939
10. Tsoro Mai Taƙama 1939-1941
11. Mai Yaƙi Muhammad 1941-1951
12. Ibrahim Maru 1951-1959
13. Baƙo Tsoho 1959-1963
14. Bube Abubakar Maru 1963-1967
15. Abdullahi Ibrahim Maru 1967-1971
16. Alh. Muhammad Mai Nasara 1971-1980
17. Alh. Ƙasimu Atiku Liman. 4/6/1980