Gwamnatin tarayya ta nada Dokta Bishir Gambo a matsayin magatakarda na Cibiyar nazarin yanayi ta kimiyya da fasaha ta Katsina.

Nadin wanda na tsawon shekaru hudu ne a matakin farko, an mika shi ne a wata wasika mai dauke da sa hannun Daraktan Ma’aikata na S.D. Mohammad, a madadin ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.

Wata sanarwa da Babban Manajan Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet), Mista Muntari Yusuf Ibrahim ya raba wa manema labarai a Abuja, ta bayyana cewa, Dakta Gambo ya yi digirin digirgir a fannin kimiyyar muhalli da kwararriya kan lalata kasa/Desertification daga Jami’ar. Botswana

Shi memba ne na Bayanin Duniya akan Hanyoyi da Fasaha (WOCAT), cibiyar sadarwa ta duniya akan Gudanar da Ƙasa mai Dorewa (SLM) wanda ke inganta takaddun shaida, rabawa da amfani da ilimin don tallafawa daidaitawa, haɓakawa da yanke shawara a cikin SLM.

Hakanan memba ne na Ƙungiyar Ƙwararrun Ƙwararrun Muhalli na Seattle, W A.

Dokta Gambo a matsayinsa na malami, ya na da wallafe-wallafe da dama da suka hada da;

Tasiri da Sarrafa Hamada a Jihohin Gabar Najeriya: Nazarin Harka a Jihar Katsina.

Tattalin Arzikin Ci Gaban Al'umma A Agroforestry: Nazari Na Karamar Hukumar Batagarawa Dake Jihar Katsina. Tasirin Hamada ga Rayuwa a Jihar Katsina, Najeriya da dai sauransu.

Dakta Gambo ya yi ayyuka da dama a ma’aikatu masu zaman kansu da na gwamnati. Wadannan sun hada da, Janar Manaja na Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KSTA); Mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Katsina kan harkokin kwadago da samar da aiki, kuma malami na wucin gadi a jami'ar Al Qalam dake jihar Katsina. Ya kuma taba zama kwamishinan ma’aikatar raya karkara, matasa da wasanni ta jihar Katsina.

Har zuwa nadin nasa, Dakta Bishir Gambo ya kasance babban mataimaki na musamman kan muhalli ga mataimakin shugaban majalisar dattawan tarayyar Najeriya.

Ana kyautata zaton Dr. Gambo zai kawowa wannan cibiya ta ilimi da gogewar da ya samu tsawon shekaru a cibiyar.

Ministan Harkokin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika ne ya kaddamar da Cibiyar nazarin yanayi ta Kimiyya da Fasaha ta Katsina a ranar 21 ga Mayu, 2019.

An kafa Cibiyar don zama cibiyar horarwa da bincike kan ilimin yanayi da canjin yanayi.