Comfort Amwe ƴar Najeriya ce kuma ƴar siyasa ce daga ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna. Tana wakiltar mazaɓar Sanga[1] a majalisar dokokin jihar Kaduna.[2]

Comfort Amwe
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Amwe ta samu takardar shaidar kammala difloma ta ƙasa (OND), a Polytechnic ta jihar Filato a shekarar 1983. Ta taɓa zama mai baiwa gwamnan jihar Kaduna shawara daga Satumba 2008 zuwa Satumba 2009.

Sana'ar siyasa

gyara sashe

Comfort Amwe ita ce shugabar ƙaramar hukumar Sanga daga watan Mayun 2010 har zuwa lokacin da ta tsaya takara kuma ta yi nasara a matsayin ƴan majalisar dokokin jihar Kaduna. Ta kasance mamba a jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP).[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-11. Retrieved 2023-03-11.
  2. https://www.shineyoureye.org/person/amwe-comfort
  3. https://sunnewsonline.com/my-pain-as-only-female-lawmaker-in-north-west-comfort-amwe/