An haifi jaruma Bilkisu Safana a Jihar Kaduna. An haife ta 5 ga watan nuwanba a shekara ta alif dari tara da tamanin da tara (1999). Tayi makarantar firamare da sakandare duk a jahar Kaduna.

Bilkisu ta shiga masana’antar kannywood a shekarun baya, Jarumar ta ci gaba da samun yabo da kuma daukaka daga masoya kallon shirin fina -finan kannywood. Bilkisu Safana na daya daga cikin fitattun jarumai mata da masana'antar kannywood ke alfahari dasu.

Ta fara wasan kwaikwayo na kannywood a matsayin 'yar rawa. Ta fito a cikin shahararrun wakokakin kannywood, tare da shahararrun mawakan kannywood, kamar Garzali Miko, Hamisu Breaker, Umar M Sharif, Sanusi Oscar, da sauran su.

Daga baya Jarumar ta shiga acikin shirin fina-finai, Ta fito a fina -finan kannywood da dama, kamar Haram, shahararren shirin fina -finan Hausa, da sauransu. [1]

Manazarta gyara sashe