Bilkisu Abdullahi

Jaruma ce a Masana'antar kanniwud ta Hausa, kyakkyawar jarumace Mai himma da kwazo da girmama na gaba da ita a masana'antar,tana daya daga cikin kyawawan mata a kanniwud, tana da dumbin masoya masu yawa.

Takaitaccen tarihin ta gyara sashe

Bilkisu an haifeta a ranar 5 ga watan mayun shekara ta 1993 a jihar lagos Dake kudancin(kudu maso yamma) najeriya mahaifin ta Dan asalin jihar Kano ne mahaifiyar ta Kuma yar jihar Adamawa ce ita ruwa biyu ne.kyakkyawa fara bafullatana.

Aure gyara sashe

Bilkisu Bata taba yin aure ba sedai tanada manema wato masu son ta da yawa.tana cikin kyawawan yan mata a masana'antar.

Karatu /masana antar fim gyara sashe

Bilkisu tayi karatun ta na firamare da sakandiri a garin Lagos, bayan , bayan rasuwar mahaifin ta Yan uwansa suka dawo da ita garin kano, tayi aiki a makarantar Dinop sakandiri school Dake hotoro kafin ta shiga masana'antar fim ta Hausa.shigan ta Masana'antar fim din ta Sami shiga ne ta hanyar babban darakta sarki Ali nuhu, fim din da ya fito da ita a kanniwud shine fim din Aikin duhu, Wanda ta fito a matsayin yar aiki. Daga Nan daukakarta ta fara inda tayi fina finai akalla 100 a kanniwud.[1][2][3]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-18. Retrieved 2023-07-18.
  2. https://www.haskenews.com.ng/2021/10/tarihin-jaruma-bilkisu-abdullahi.html?m=1
  3. https://ng.linkedin.com/in/bilkisu-abdullahi-19840822a