Almara labari ne, ko tambaya ta sigar wasa ƙwaƙwalwa, Ɗangambo ya bayyana Almara da labarin da ke jefa tambaya a cikin ƙwaƙwalwan mai saurare.[1]

Almara zance ne wanda hausawa sukeyi alokacin nishadi ko kuma wasa kwakwalwa.

Rabe-Raben Almara gyara sashe

A dunƙule, masana harshen Hausa sun kasa almara zuwa gida biyu:

  1. Almarar Wasa Ƙwaƙwalwa: ita ce almarar da ke ɗauke da labarin da ke ɗauke da matsalar da bayan an gama bayar da shi za a buƙaci masu sauraro su warware matsalar. Misali, wata rana, wata budurwa ta je zance wajen saurayinta da ya ke wani gari. Da suka gama zance, dare ya yi, sai ya tafi zai raka ta. A tsakanin waɗannan garuruwa guda biyu, akwai wani kogi. Da suka isa bakin wannan kogi, sai saurayin ya ce budurwar ta dakata, ya iya ruwa, shi zai fara haura kogin ya ɗauko kwale-kwale don ya haye da ita. Sai ya shiga ruwa, sai da ya je tsakiyar ruwan, sai wani ƙaton kada ya biyo shi zai kama shi, da ƙyar ya samu ya haye. Bayan ya haye, sai ya hango kura ta rugo da gudu za ta cinye wannan budurwar tasa. To, wai idan kai ne wannan saurayin ya zaka yi? Za ka shigo ruwa kada ya cinye ka ne, ko kuwa za ka tsaya kura ta cinye budurwar taka?
  2. Almarar Raha: almara ce da ake yin ta ta hanyar bayar da labarin bandariya, wacce kuma ba ta ɗauke da wata matsalar da a ƙarshe za a nemi mai sauraro ya warware ta.

Akwai kamanceceniya tsakanin almara da tatsuniya. Sai dai, babban abin da ke bambanta tsakaninsu su shi ne cewa, an fi gina almara da sunayen mutane, wato ba a cika gina zunzurutun labarin almara da sunayen wasu halittu zalla ba batare da mutum ya shigo ciki ba.

Bibiliyo gyara sashe

  • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
  • ·Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
  • ·The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.

Manazarta gyara sashe

  1. Furniss,Graham. (1996). Poetry,prose and popular culture in Hausa.p.57